An damke 'yan Boko Haram 14 a Niger

Matasan Diffa da ke yi wa Boko Haram aiki
Bayanan hoto, Matasan Diffa da ke yi wa Boko Haram aiki

Rahotanni daga Jamhuriyar Niger na cewar an damke 'yan Boko Haram su goma sha hudu a yankin Diffa na kasar bayan sun kaiwa jami'an tsaro hari.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata a Diffa mai makwabtaka da Nigeria inda ake samun rikicin 'yan Boko Haram.

Dubban 'yan Nigeria da suka tserewa rikicin Boko Haram a Nigeria sun tsallaka yankin Diffa ne domin neman mafaka.

A cikin makonnin da suka wuce ne BBC ta gano cewar kungiyar Boko Haram na daukar mayaka daga yankin Diffa inda take biyansu kudi don su yi mata aiki.

Hukumomi a Nigeria sun bukaci gwamnatocin makwabtan kasashe sun taimaka wajen yaki da kungiyar Boko Haram musamman a garuruwan kan iyakar kasar.