Gwamnoni uku sun ziyarci Borno

Kashim Shettima, gwamnan jihar Borno

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Kashim Shettima, gwamnan jihar Borno

Gwamnonin jihohin Bauchi, da Gombe da Taraba sun ziyarci jihar Borno domin nuna goyon baya ga jama'ar jihar da kuma yin jaje saboda tashin hankalin da jihar take fuskanta.

Gwamnonin sun bayyana takaici dangane irin asarar rayukan da aka yi a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa cikin 'yan makonnin nan.

Gwamnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda wanda ya jagoranci ziyarar ya ce, zasu ci gaba da tallafawa juna domin tabbatar da kare rayuka da dukiyar jama'a.

Gwamnonin uku sun kuma yi kira ga jama'a da su rika taimakawa jami'an tsaro da bayanai a duk lokacin da suka ga wani abu.

Gwamnonin Ibrahim Dankwambo na Gombe, da Garba Umar na Taraba sun nuna taikaci dangane da yadda taɓarɓarewar tsaro ke kawo koma baya a yankin arewa maso gabas.