An ce 'Yan Boko Haram sun yanka mutane a hanyar Banki

Asalin hoton, AFP
A Najeriya, wasu rahotanni sun ce an kashe mutane da dama a wani hari da ake kyautata zaton cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai da safiyar yau a jihar Borno.
Rahotannin sun ce maharan sun tare kan babbar hanyar ce inda suka yi ta fitar da jama'a a cikin motocin da suke ciki suka kuma hallaka su.
Wannan hari dai na zuwa ne bayan wani harin da aka kai a daren jiya a garin Bama da kuma wanda aka kai kan gidan wani janar din Sojin kasar dake birnin Maiduguri, inda aka halaka soja daya tare da raunata wasu mutane hudu.







