Mu muka kashe Sheikh Albani - Shekau

Asalin hoton, AFP
Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin cewar ita ce ta hallaka sanannen Malamin addinnin musulunci na Zaria, Sheikh Mohammed Auwal Adam Albani.
Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ta fitar, inda Shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya yi jawabi.
An dai kashe Sheikh Albani ne tare da uwargidansa da kuma dansa a wani hari da aka kai musu a Zaria.
Kungiyar ta Boko Haram ta kuma ce ita ce ke da alhakin hare haren baya bayan nan da aka kai musamman a jihar Borno.
A cewar Abubakar Shekau, kungiyar za ta kaddamar da hari kan wasu manyan 'yan siyasa a Nigeria wadanda ke goyon bayan demokradiya.







