Taliban ta kama karen Amurka na 'leken asiri'

Asalin hoton, Reuters
Kungiyar Taliban ta ce ta kama wani kare na dakarun sojin Amurka da ke aiki a gabashin Afghanistan.
Wani hoto da aka wallafa a shafin Twitter ya nuna wani dan kwikwiyo mai launin ruwan kasa sanye da bakar laya a wuya.
Kungiyar ta Taliban ta ce ta kama karen, wanda ake yi wa lakabi Kanal, yayin da aka kai wani samame da daddare a watan Disamba yana dauke da karamar kamara da na'urar da ke tantance inda mutane suke.
Taliban ta kuma nuna makaman da ta kwace lokacin samamen -- yawancinsu irin wadanda dakarun Amurka na musamman ke amfani da su ne.






