Hukumar SSS ta saki Nasir El-Rufa'i

Hukumar tsaro ta farin kaya a Nigeria, SSS, ta saki mataimakin sakataren jam'iyyar adawa ta APC, Malam Nasir El-Rufa'i bayan da ya kwashe sa'o'i 15 a hannunta sakamakon amsa gayyatar da ta yi ma sa.
Hukumar ta SSS ta gaiyaci Malam El-Rufa'i ne domin amsa tambayoyi game da kalamin da ake rawaito ya ce za'a zubar da jini a Nigeria matukar ba a yi adalci a zabukan 2015 ba.
El-Rufa'in dai ya ce wannan zance ba ingiza tashin hankali ba ne, illa tunatarwa game da irin rikice-rikicen da su ka biyo bayan zabubbukan da aka gudanar a kasar a baya.
Sai dai jam'iyyar ta APC ta yi Allah-wadai da gayyatar ta SSS in da ta yi zargin cewa gwamnati na amfani da hukumar da nufin karya-lagon 'yan adawa.







