El-Rufa'i ya amsa gayyatar SSS

Mataimakin sakataren jam'iyyar APC, Malam Nasir el-Rufai
Bayanan hoto, Mataimakin sakataren jam'iyyar APC, Malam Nasir el-Rufai

Mataimakin sakataren jam'iyyar adawa ta APC, Malam Nasir el-Rufa'i ya kai kansa hukumar tsaro ta SSS ta yi masa bisa zargin iza wutar tashin hankali, bayan da a baya ya ce ba zai amsa gayyatar ba.

Hukumar SSS dai na neman el-Rufai bisa furucin da ake zargin ya yi cewa idan har ba a yi adalci a zaben 2015 ba, za a zubar da jini a Nigeria.

El-Rufai, wanda ya je ofishin SSS tare da rakiyar gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya ce ya amsa gayyatar ne bisa shawarar lauyoyinsa da kuma shugabannin jam'iyyarsu ta APC.

Ya kuma ce tabbas maganar da ake zargin ya fada haka take, kuma ba ingiza kowa ya ke ba illa gargadi bisa la'akari da abin da ya faru a zabubbukan baya.

Kawo yanzu dai hukumar SSS ba ta ce komai ba game da ziyarar ta el-Rufai da kuma furucin na sa.