UN: Boko Haram na aikata laifukan yaki

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Boko Haram matsoraciya ce
Bayanan hoto, Majalisar Dinkin Duniya ta ce Boko Haram matsoraciya ce

Hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mai yiwuwa a sanya kungiyar Boko Haram a cikin kungiyoyin da ke aikata laifukan yaki.

Kakakin hukumar, Cecile Pouilly, ta ce "idan aka hakkake cewa mambobin kungiyar Boko Haram da takwarorinta sune ke kai hare-haren da ake kai wa fararen hula, hakan zai zama laifin cin zarafin bil Adama.''

Hukumar ta kuma yi Alla-wadai da harin da 'yan kungiyar suka kai wa wasu mutane da ke kan hanyarsu ta dawowa daga wajen daurin aure a jihar Borno da ke Nigeria.

Harin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Pouilly ta kara da cewa hare-haren da Boko Haram ke kai wa fararen hula da 'yan siyasa da ma'aikatan kasashen waje da makamantansu sun nuna cewa kungiyar matsoraciya ce.

A baya bayan nan dai 'yan kungiyar sun kai wani harin a kan babura da motocin a-kori-kura, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka mutane da dama.