An sauko daga hawan Arafat

Mahajjata a Saudi Arabiya sun tashi daga tsayuwar Arafat, ibada mafi muhimmanci a rukunan aikin hajji.
Kimanin Musulmai miliyan daya da dubu 300 ne daga sassan duniya ke yin ibadar aikin Hajji a kasar Saudiyya.
Mahajjatan dai sun kwashe tsawon yinin yau a farfajiyar filin na Arfat, suna ibada tare da addu'oi har zuwa faduwar rana.
Aikin Hajji dai na daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar, kuma wajibi ne ga kowane musulmi da ke da hali sau daya a rayuwarsa.
Kimanin maniyyata dubu saba'in da biyar ne daga Najeriya suke gudanar da aikin Hajji a bana.






