Dangote zai gina katafaren asibiti a Kano

Gidauniyar Dangote za ta gina katafaren asibiti mai gadaje 1,000 a jihar Kano dake arewacin Najeriya.
Shugaban gidauniyar, Alhaji Aliko Dangote ya sanar da hakan ne a lokacin bikin aza tubalin ginin wani dakin tiyata mai cin mutane 12 a asibitin Murtala dake Kano.
Gidauniyar za ta kashe naira biliyan biyu wajen gina asibitin don taimakon 'yan kasar wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya.
A cewarsa, matakin zai rage yawan 'yan Najeriya dake zuwa kasashen waje don neman magani.
Gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso a wajen bukin ya ce matakin zai taimawa al'ummar jihar musamman ganin cewar ana bukatar karin asibitoci da kula da lafiyar al'umma.
Gwamnan babban bankin Najeriya-CBN Sanusi Lamido Sanusi, ya ce 'yan Najeriya na kashe kusan naira biliyan tamanin a duk shekara wajen neman lafiya a kasashen waje.







