Shirin soma taron Majalisar Dinkin Duniya

A yau ake shirin soma babban taron majalisar dinkin duniya a birnin NewYork na Amurka.
Rikicin Syria da dangartakar Iran tare da Kasashen yamma ne zasu mamaye tattaunawa a taron.
Shugaba Barack Obama na Amurka da sabon Shugaban Iran Hassan Rouhani zasu gabatar da jawabi ga taron.
Fadar white house tace ba a fidda ran wata ganawa ba, tsakanin shugabannin biyu, wacce ita ce irinta ta farko tun juyin juya halin Kasar.
A waje daya kuma sakataren Amurka John Kerry zai gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov domin kokarin warware bancance bancancen dake tsakaninsu kan yadda za a tabbatar da cewa Syria ta mika makamanta masu guba.







