'Yan tawayen sun amince su tsagaita wuta

Kungiyoyin 'yan tawaye biyu, sojojin Syria da suka sauya sheka da kuma Jihar Musulunci a Iraq da Syria, sun amince su tsagaita wuta a garin Azaz, bayan shafe kwanaki suna fafatawa a tsakaninsu.
Kungiyar Jihar Musulunci wacce ke da alaka da kungiyar AlQaida, ta kwace garin Azaz dake arewacin kasar a ranar Laraba, daga hannun babbar kungiyar sojojin da suka sauya sheka na Syria dake samun goyon bayan kasashen yamma.
Fadan tsakanin kungiyoyin biyu ya janyo fargabar barkewar wani rikici, a tashin hankalin da Syria ke fama da shi.
Wakilin BBC yace bangarorin sun amince su yi musayar fursunoni, su kuma mayar da abubuwan da suka kwace.







