Rouhani ya yi tayin sa baki a Syria

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya nuna aniyar gwamnatinsa ta taimaka wa wajen tabbatar da zaman lafiya a Syria.
A abin da ya kira manufarsa ta tattaunawar ci gaba da sauran kasashe.
A wata kasida da ya wallafa a jaridar Washington Post.
Mr Rouhani ya bukaci kasashen duniya su yi amfani da zabensa tare da Iran su kawo karshen gabar da ke ruru wutar rikici a Gabas-ta-tsakiya.
Jami'an fadar gwamnatin Amurka sun ce a shirye Shugaba Obama yake ya gana da Mr Rouhani.







