Syria: 'An gabatar da rahoton son zuciya'

Syria ta baiwa Rasha wasu sabbin shaidun dake nuna cewa 'yan tawaye ne suka yi amfani da makamai masu guba a harin ranar 21 ga watan Agusta.
Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov ne ya bayyana hakan.
Mr. Ryabkov wanda ya ziyarci Damascus a daren ranar Talata, ya ce gwamnatin Syria ta gabatar da kwararran hujjojin da kwararrun Rasha suka amince dasu.
Rasha ta zargi masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya a kan samar da rahoto na son zuciya na bangare daya a kan amfani da makamai masu guba a Syria.
Mr. Ryabkov ya nuna takaici game da kin ziyartar wurare uku da masu bincike suka yi.







