An rantsar da sabon Fira Ministan Australia

An rantsar da Sabon Prime Ministan Australia Tony Abbott, bayan nasarar daya samu a zaben da aka gudanar cikin wannan wata.
Mr Abbott wanda yake jagorantar wata hadaka yace abubuwan da zai baiwa mahimmanci sune soke wani haraji akan gurbataccen hayakin da ake fitarwa, da kuma rushe hukumar kula da canjn yanayi ta Australian.
Ya kuma ce shirinsa na hana masu neman mafaka isowa ta hanyar jirgin ruwa daga Indonesia, zai soma aiki nan take.
Ana dai sukar Mr Abbott saboda sanya mace kwaya daya tak a cikin majalisar ministocinsa.







