Muna kan bakanmu a kan Syria —Putin

China da Rasha na goyon bayan Shugaba Assad
Bayanan hoto, China da Rasha na goyon bayan Shugaba Assad

Amurka da Rasha ba su warware bambancin da ke tsakaninsu ba a kan batun amfani da matakin soji a kan Syria, kamar yadda Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana.

Mista Putin ya ce ba daidai ba ne a gudanar da wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Ya bayyana haka ne a taron manena labarai a rana ta karshe na taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 a St Petersburg.

Shugaban Amurka, Barack Obama ya neman goyon bayan shugabannin kungiyar G20 a kan yinkurin kasarsa na yi wa Syria luguden wuta.

Amurka na zargin Shugaba Bashar al-Assad da kashe mutane 1,429 da makami mai guba a Damascus a ranar 21 ga watan Agusta.