Kasashen G20 na tattaunawa kan Syria

Taron G20
Bayanan hoto, Taron G20

Shugabannin kungiyar G20 ta kasashe masu cigaban masana'antu dake taro a birnin St Petersburg na Rasha, suna tattaunawa kan rikicin Syria, a lokacin liyafar cin abincin daren da aka shirya ma su a ranar farko ta taron.

Wani wakilin BBC ya ce, Rasha, mai daukar bakuncin taron, tana adawa matuka da duk wani matakin soja da Amurka ke son dauka a kan kasar ta Syria, bisa zargin amfani da makamai masu guba.

Ya ce shugabanni da dama ba sa goyon bayan daukar matakin soja a kan Syriar ba tare da amincewar Majalisar Dinkin Duniya ba.

Shugaban Amurka, Barack Obama, ya tattauna da takwaransa na Japan a kan batun na Syria, kuma yana ta kokarin samun goyon baya domin yin amfani da karfin soja a kan gwamnatin Bashar al-Assad.

A wani mataki da ake gani a matsayin adawa da kiran da Amurka ke yi domin a yi amfani da karfin soja a kan Syria, Paparoma Francis ya aikewa da shugaban Rasha wasika, yana mai yin kira ga shugabannin kasashen duniya su kawar da yunkurin yin amfani da karfin soja kan Syria.

Can kuma a Syriar akalla mutane 4 sun rasa rayikansu, wasu karin 6 kuma suka samu raunuka, a wani harin bam da aka dana cikin mota a yammacin birnin Damascus.

Wasu rahotannin sun ce tsohon ministan tsaron Syriar, Janar Ali Habib, ya isa Turkiya, bayan da ya canza sheka.

Ya dai yi murabus ne a shekara ta 2011.