Putin ya gargadi Amurka a kan Syria

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gargadi Amurka da kawayenta kada su yi gaban kansu su dauki mataki a kan Syria.
A cewarsa, daukar matakin soji ba tare da amincewar Majalisar Dinkin Duniya ba, cin zali ne.
Mista Putin ya ce zai iya goyon bayan daukar matakin soji a kan Syria idan har aka tabbatar da cewar gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba.
Shugaban Amurka, Barack Obama ya yi kira a dauki kwakwarar mataki a kan Syria bisa zargin ta yi amfani da makami mai guba a kan 'yan kasarta.
A ranar Talata ne wakilan kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattijan Amurka suka amince da wani daftarin da ke nuna goyon bayan amfani da karfin soji a kan Syria.







