Faransa na kokarin kafa hujja kan Syria

Jean-Marc Ayrault
Bayanan hoto, Jean-Marc Ayrault

Yanzu haka dai kasashen duniya suna ta kai-kawo a kan Syria, don ganin yadda za a yi da ita, bayan daruruwan mutane sun hallaka a kwanan nan a kusa da birnin Damascus, sakamakon harin da ake jin na makamai masu guba ne.

Ko da yake har yanzu ana jiran rahoton sufetocin majalisar dinkin duniya da suka ziyarci kasar don tattara shaidu, tuni wasu kasashen irinsu Amirka da Faransa suka hakikance cewa, gwamnatin Syriar ce ta yi amfani da makaman masu guba.

Nan gaba a ranar Litinin Pirayi ministan Faransa, Jean-Marc Ayrault , zai gabatar wa shugabannin majalisar dokokin kasar bayanan sirrin da ke tabbatar da zargin.

Yayin da ita kuma fadar gwamnatin Amirka, ke neman goyon bayan 'yan majalisar dokokin kasar, kan batun daukar matakan soja a kan Syriar.

'Martani daga Assad'

Gwamnatin Syria ta yi gargadin cewa duk wani matakin soji da Amurka za ta dauka kan kasar, tamkar bada goyon baya ne ga kungiyar Al-Qaeda da rassanta.

Mataimakin Ministan harkokin waje na Syrian Faisal Mekdad ya shaidawa BBC cewa, gungun mutanen dake dauke da makamai da Amurka ke marawa baya, su ne suka yi amfani da makamai masu guba amma ba gwamnatin Syria ba.

Harin dai wanda aka kai a Damascus ya hallaka sama da fararen hula 1400.