Neman daukar mataki game da harin Syria

Kasashen Birtaniya da Faransa da Turkiyya sun fara kira ga kasashen duniya da a dauki kwakkwaran martani, game da makamai masu guba da aka kai hari da su a Syria, a ranar Laraba.
Masu fafutuka na bangaren 'yan adawa dai sun ce harin ya kai ga mutuwar daruruwan mutane.
Birtaniya na kira da a baiwa masu binciken makamai na Majalisar Dinkin Duniya, wandanda suke kasar damar zuwa gurin da aka kai harin cikin gaggawa.
Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius ya ce idan an tabbatar da amfani da makaman masu guba, to yakamata a dauki mataki na soji.
Sai dai babu wani alamu na cewa za a bar masu binciken makaman su je gurin da aka yi ta'asar, saboda 'yarjejeniyar da aka cimma da gwamnatin ta Syria ita ce, za su ziyarci gurare uku ne kawai.







