'An kashe mataimakin Abubakar Shekau'

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau
Bayanan hoto, Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Shalkwatar tsaro ta Najeriya ta tabbatarwa BBC cewa dakarun tsaron kasar sun kashe mutum na biyu mai girman mukami a kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram a farkon wannan watan.

Rundunar tsaron ta ce ta kashe Momodu Bama ne a wani ba-ta-kashi da aka yi, yayin dakile wani hari da 'yan kungiyar ta kai, a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Wata sanarwa da kakakin JTF a jihar Borno, Laftanar Kanar Sagir Musa ya fitar, ta ce Momodu Bama wanda ake yiwa lakabi da Abu Sa'ad, shi ne mataimakin Imam Abubakar Shekau.

A baya, gwamnatin Najeriya ta dauki alkawarin bada tukwicin dalan Amurka dubu ashirin da biyar ga duk wanda ya taimaka da bayannan da za su taimaka wajen damke Momodu Bama.