Obama ya soke ganawarsa da Putin

Shugaba Obama da Shugaba Putin
Bayanan hoto, Shugaba Obama da Shugaba Putin

Shugaba Barack Obama ya soke tattaunawar da ya shirya yi tsakaninsa da Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin a Moscow cikin wata mai zuwa.

Ana ganin wannan mataki a matsayin maida martani ga shawarar da gwamnatin Rasha ta yanke, na bada mafaka ga tsohon jami'in leken asirin Amurka Edward Snowden.

To sai dai mahukunta a Amurkar sun ce, Shugaba Obama bai jingine shirinsa na halartar taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 ba, wanda za a yi a St. Petersburg a watan Satumba.

A ranar Talata,Mista Obama ya bayyana cewar ya ji takaicin matakin Rasha na barin Mista Snowden ya zauna a cikin kasarta.