Sojojin Siriya sun kwace birnin Homs

An yi luguden wuta a Homs
Bayanan hoto, An yi luguden wuta a Homs

Sojojin gwamnatin Siriya sun kwace iko da galibin yankunan Khalidiya dake tsakiyar birnin Homs.

Wata tashar Talabijin ta larabci al-Mayadeen ta nuna wasu hotuna wadanda ta ce an dauka a yankin wanda ya nuna mummunan ta'adin da aka yiwa gine-gine da tarin buraguzai da kuma kankare da suka rugurguje.

Tashar talabijin din ta ce kusan kashi tamanin cikin dari na yankin yana karkashin sojojin gwamnati.

Masu fafutuka su ma sun tabbatar da labarin inda suka ce tsohon garin Homs ne kawai da wasu yan larduna a birnin suke karkashin ikon yan tawaye.