'Yan bindiga sun kashe mutane uku a Darazo

Hukumomin tsaro a jihar Bauchi dake arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane uku ciki har da jami'in tsaro da karamar yarinya.
Hakan ya biyo bayan harin da wasu 'yan-bindiga suka kai a caji-ofis na 'yan-sanda, da wani banki da kuma wani Gidan Mai, a garin Darazo dake arewacin jihar.
Maharan dai sun far wa garin ne a daren ranar Litinin, inda suka kwashe lokacin mai tsawo suna bata-kashi da jami'an tsaro.
Kwamishinan 'yan sanda a jihar ta Bauchi, Muhammad Ladan, ya tabbatar wa da BBC mutuwar mutane uku a lamarin.
Harin ya firgita jama'ar garin na Darazo musamman yadda aka shafe fiye da sa'a guda ana musayar wuta da bindigogi tsakanin maharan da kuma jami'an tsaro.







