Sir Alex Ferguson zai yi ritaya

Kulob din kwallon kafa na Manchester United ya bada sanarwar cewa manajan club din, Sir Alex Ferguson zai yi ritaya a karshen kakar bana ta wasan kwallon kafa.
Sir Alex Ferguson shine manajan da ya fi kowanne samun nasara a tarihin wasan kwallon kafa na Birtania.
Tun daga lokacin da ya shiga Club din a shekara ta 1986, ya lashe kofin zakarun turai sau 2, kofin gasar Premier sau 13 da kuma kofin FA sau 5.
A wata sanarwa da aka fitar, Sir Alex ya ce wannan shine lokacin da ya fi dacewa ya ajiye aiki a lokacin da Club din ya ke da babban matsayin da zai iya samu.
Zai ci gaba da zama a Club din na Manchester United a matsayin Direkata da kuma Jakada.






