Xi Jinping na son karawa sojin Sin karfi

Sabon Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara wa sojojin kasar karfi tare da cusa musu da'a da kwarin-gwiwar samun nasara a yaki.
Lokacin da yake magana a karshen taron shekara-shekara na jam'iyyar National Peoples Congress, Xi Jinping ya ce, zai yi yaki a kan abinda ya kira farfado da martabar kasar China.
'Yace, bunkasar tattalin arziki shine zai cigaba da zama abu mafi muhimmanci a gwamnatinsa.
Haka kuma ya yi alwashin tsarkake gwamnati, ya kuma ce akwai bukatar rage gibin dake tsakanin mutanen China.







