Amurka za ta janye sojoji daga Afghanistan

Shugaban Amurka, Barack Obama, ya ce kasar za ta janye sojojinta guda dubu talatin da hudu daga kasar Afghanistan a badi.
Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabinsa na farko ga 'yan kasar tun bayan zaben da aka yi masa a wa'adi na biyu.
Mista Obama ya ce tuni Amurka ta dawo da dakarunta guda dubu 33 gida daga Afghanistan, yana mai cewa a yanzu dakarun kasar za su rika taka rawa ce kawai a matsayin masu bayar da taimako ga sojojin Afghanistan.
Jawabin Mista Obama ya tabo batutuwa da dama, wadanda suka shafi yadda za a gina tattalin arzikin Amurka.
Ya ce Amurka za ta kammala kulla yarjejeniyar kasuwanci tsakanin ta da kasashen da ke nahiyar Asia.
A cewarsa, hakan zai bayar da dama a bunkasa yadda Amurka ke fitar da kayayyaki kasashen waje sannan a samarwa 'yan kasar karin ayyukan yi.







