Maiduguri: 'Yan bindiga sun 'yanka' mutane 5

A Najeriya, rahotanni na cewa wadansu mutane da ba a san ko su wanene ba sun kai hari birnin Maduguri na jihar Borno dake arewacin kasar, inda suka 'yanka' mutane biyar.
Mazauna birnin dai sun ce lamarin ya faru ne a jiya da daddare, kuma tuni jami'an tsaro suka kwashe gawarwakin mutanen da aka kashe.
Rudunar dake aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar, wato JTF, ta tabbatar da aukuwar lamarin, koda yake ta ce mutane uku ne aka kashe.
Jiya ma dai an bada rahotannin kisan wasu mutane a kasuwar Damboa dake jihar ta Borno.
Koda a watan Yulin bara wasu da ba a san ko su wanene ba sun yanka wasu Indiyawa biyu a garin na Maiduguri.
Maiduguri gari ne da yake fama da hare-hare da masu nasaba da kungiyar nan da ake kira Boko Haram.







