Mokhtar Belmokhtar ya dau alhakin rikicin Aljeriya

An bada rahotan cewa mai kaifin kishin Islamar nan dan Algeria da ake zargin shine ya bada umarnin kai hari kan matatar iskar gas- Mokhtar Belmokhtar- ya tabbatar da cewa yana da hannu a ciki.
Ya yi magane ne a wani a wani sakon bidiyo da shafin Intanet na kafar yada labaran kasar Mauritania wata 'Sahara Media' ya gani
A cikin bidiyon Mokhtar Belmoktar ya bukaci a kawo karshen hare haren da sojojin Kasashen duniya suke kaiwa masu kaifin kishin Islama a Mali
'Sahara Media' dai tace an nadi bidiyon ne a makon da ya gabata, a lokacin da ake garkuwa da mutanen a Algerian







