Obama ya zabi sabon Ministan tsaro

Shugaba Barack Obama ya zabi tsohon dan majalisar dattawa na jam'iyyar Republican, Chuck Hagel a matsayin sabon Ministan tsaron Amurka.
Mr Obama ya ce Hagel ya samu lambar yabo bisa rawar da ya taka da kwazon da ya nuna ya yin yakin Vietnam.
Mr Obama ya ce Chuck ya san cewa yaki ba wasan yara ba ne, ya kuma fahimci cewa tura matasan sojojin Amurka yaki da zubar da jininsu abu ne da ake yi idan matukar bukatar hakan ta taso.
Shugaba Obama ya kuma ce ya zabi mai ba shi shawara a kan al'amuran yaki da ta'addanci, John Brennan, don ya jagoranci hukumar leken asiri ta CIA.







