Taliban za ta yi sulhu da Northern Alliance

Mayakan kungiyar Taliban a Afghanistan
Bayanan hoto, Mayakan kungiyar Taliban a Afghanistan

Jagororin kungiyar Taliban a Afghanistan za su hau teburin shawarwari da tsofaffin abokan gabarsu na kungiyar Northern Alliance.

Wakilan shugaban kungiyar Taliban, Mullah Omar, za su yi wata tattaunawa ta sirri ne a Paris da jagororin kungiyar ta Northern Alliance da kuma jami'an gwamnatin Afghanistan.

Kungiyar ta Northern Allinace ce dai ta taimaka wajen fatattakar gwamnatin Taliban yayin mamayar da Amurka ta jagoranta a shekarar 2001.

Ana kyautata zaton tattaunawar bangare ne na kokarin da Taliban da sauran bangarorin kasar ta Afghanistan ke yi, don shirya wa janyewar dakarun kungiyar tsaro ta NATO.