An kashe wani dan jarida a Rasha

Wani dan jaridar talabijin na Rasha da aka harbe har lahira ya zamo dan jarida na baya-bayan nan da aka kashe a kasar.
Kazbek Gekkiyev, dan shekaru 26, mai karanta labarai ne a gidan talabijin mallakar jamhuriyar Kabardino-Balkaria.
Hare-hare kan ‘yan jarida ba bakon abu bane a Rasha. Kuma yankin North Caucasus shi ne yankin da ya fi kowanne fama da tashin hankali, inda jami’an tsaro ke yakar kungiyoyin Islama.
A ranar Alhamis an raunata mataimakin ministan sufuri na Kabardino-Balkaria a wani harin bam.
Jami’in Vladislav Dyadshenko, an tafi da shi asibiti ne bayan da wasu abubuwa suka fashe a kusa da motarsa a Nalchik, babban birnin yankin.
‘Kisan gilla’
Gekkiyev, an kashe shi ne a birnin bayan da ya dawo daga wurin aiki ranar Laraba da daddare.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce wasu mutane ne suka tsayar da dan jaridar a kan titi.
Rahotanni sun ce sun tantance sunansa ne da aikinsa, sannan suka bude masa wuta.
Wannan kisan dai ya yi kama da irin kasha-kashen gillar da ake yi wa ‘yan jarida a kasar ta Rasha.











