Ƙin jinin Musulmai ya ƙaru a duniya

Wasu alkaluma da BBC ta gani sun nuna cewa an samu karuwar sakonnin Twitter na ƙin jinin Musulmai da ake aikawa da harshen Ingilishi a duniya.
Haka kuma akasarin sakonnin sun fito ne daga Burtaniya.
Masu sharhi na kungiyar masana a Burtaniya sun gano cewa, an aika da sakonnin tozartarwa da ƙiyayya a kan musulmai kusan 7,000 a kullum, a cikin watan Yulin da ya gabata.
Alkaluman sun kai kololuwa idan aka hada da irin wadannan sakonnin 2,500 da aka aika a watan Afrilun da ya wuce.
Yayin da a ranar 15 ga watan Yuni aka aika sakonnin Twitter 21,190, bayan kai hari da babbar mota a kasar Faransa lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 80.
Kungiyar da ke da'awar kafa daular Musulunci ta IS ce ta dauki alhakin kai hari na birnin Nice.







