An tsare Shah Rukh Khan a Amurka

Mutane sun bayana rashin jin dadinsu kan lamarin

Asalin hoton, TWITTER

Bayanan hoto, Mutane sun bayana rashin jin dadinsu kan lamarin

Fitaccen dan wasan kwaikwayo na Indiya Shah Rukh Khan ya nuna matukar bacin ransa kan tsare shi da aka yi a filin jiragen saman Los Angeles da ke Amurka.

Babu cikakken bayan kan abin da ya sa aka tsare shi da ma tsawon lokacin da ya yi a tsare.

Sai dai jakadan Amurka a Indiya ya nemi gafarsa, yana mai cewa hukumomi a Amurka na yin bakin kokarinsu domin ganin hakan bai sake faruwa ba.

A shekarar 2012, an tsare Khan tsawon minti 90 a filin jiragen saman White Plains da ke kusa da birnin New York.

Kazalika, a shekarar 2009 an dakatar da shi tsawon awa biyu a filin jirgin saman Newark.

Sai dai an sallame shi bayan ofishin jakadancin Indiya ya sanya baki.