Kasuwar 'yan kwallon kafa: Makomar Ronaldo, Werner, Neymar, Winks, Raphinha, Rodriguez, Umtiti, De Ligt, Lewandowski

Ana hasashen cewa Chelsea na son sanya dan wasan Jamus Timo Werner, mai shekara 26, cikin yarjejeniyar musayar da za ta ba ta damar daukar dan wasan Juventus da Netherlands Matthijs de Ligt, mai shekara 22. (Sky Sports)
Dan wasan Manchester United da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, na daya daga cikin batutuwan da aka tattaunawa lokacin da sabon mamallakin Chelsea Todd Boehly ya gana da wakilin dan wasan Jorge Mendes a makon jiya. (The Athletic - subscription required)
Roma na son daukar Ronaldo tare da sake hada shi da tsohon mai gidansa a Real Madrid, Jose Mourinho. (Retesport - in Italian)
Everton da Tottenham na ci gaba da tattaunawa kan musayar dan wasan tsakiya na Ingila Harry Winks, mai shekara 26. (Sky Sports)
Juventus da PSG sun fara tattaunawa kan dauko dan wasan gaba na Brazil Neymar, mai shekara 30, wanda shi ma ake hasashen zai tafi Chelsea. (AS - in Spanish)
Manchester United na fama da bashin fam miliyan daya, idan ba su ci gaba da shirin sabunta kungiyar kungiyarOld Trafford. (Mirror)
Arsenal na kokarin rattaba hannu kan yarjejeniyar dauko dan wasan Leeds United kuma na gaba a Brazil Raphinha, da ake sa ran kulob din na Landan zai dauki matashin dan wasan mai shekara 25. (The Athletic- subscription required)
Manajan Chelsea, Thomas Tuchel yana tuntubar dan wasan gaba na Manchester City da England Raheem Sterling, mai shekara 27. (The Telegraph)
Tsohon dan wasan tsakiya na Everton, James Rodriguez, mai shekara 30, na son sake buga kwallo a Turai, idan Colombia ta bar bangaren Qatar. (Fabrizio Romano)
An bukaci mai tsaron baya na Middlesbrough Djed Spence, mai shekara 21, ya bar kulob din, ba tare da an cimma yarjejeniya amincewa komawarsa Tottenham. (Football.London)
Mai tsaron baya na Barcelona Samuel Umtiti, dan shekara 28, zai bar kulob din a kakar wasa ta bana, tare da Girona, da wasu daga cikin 'yan Siri A 'yan kungiyar kwallon kasar Faransa.(Ekrem Konur)
Leeds United na shirin kashe fam miliyan 26, domin dauko dan wasan Bruges, kuma na gaban Belgium, Charles de Ketelaere, nai shekara 21. (Mail)
Bayern Munich taki amsa kiraye-kirayen dauko dan wasan gaba na Barcelonada Poland Robert Lewandowski, mai shekara 33, a kokarin rike shi a kulob. (Sport - in Spanish)











