An bankado tarin almundahana kan Jacob Zuma

Jacob Zuma

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A yanzu haka tsohon shugaba Jacob Zuma yana gidan yari

Babban Alkalin Afirka ta Kudu ya soki jam'iyyar ANC mai mulkin kasar da cewa ta samar da yanayin da ya bayar da gagarumar dama ta cin hanci da rashawa da wawashe dukiyar gwamnati a lokacin mulkin tsohon shugaba Jacob Zuma.

Haka kuma Babban Mai Shari'ar ya ce idan da jam'iyyar ta dauki mataki da wuri a kan mummunar alakar da ke tsakanin Mista Zuma da abokan huldarsa, iyalan gidan Gupta, da ta taimaka wajen kare biliyoyin kudi da gwamnatin kasar ta yi asara.

Duka wannan na cikin rahoton karshe ne na binciken cin hanci da rashawa da almundahana da aka yi wa gwamnatin tsohon Shugaba Zuma.

An dai fitar da wannan rahoto na karshe ne a kan binciken almundahanar da aka tafka a lokacin mulkin na tsohon shugaban Afirka ta Kudun, Jacob Zuma, bayan bincike na tsawon shekara hudu.

.

Asalin hoton, Getty Images

Rahoton, wanda hukumar da Alkalin alkalan kasar, Raymon Zondo, ke jagoranta ta fitar yana dauke ne da tarin bayanai da ke nuna yadda tsohon shugaban kasar da makusanta, kuma abokan huldarsa na kut da kut, sanannun nan iyalan Gupta suka wawashe lalitar kasar.

Abin da dukkaninsu suka musanta, cewa sun aikata wani abu da ba daidai ba.

Haka kuma binciken ya bayyana cewa Mista Zuma tare da hadin kan tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasar, Arthur Fraser, sun dakatar da wani bincike kan harkokin iyalan na Gupta a shekarar 2011, abin da ya bayar da damar wawason arzikin kasar.

Harwayau, rahoton mai shafi sama da dubu biyar, ya bankado yadda iyalan na gidan Gupta suka kasance da tasiri sosai wajen nadi da kuma korar ministocin gwamnatin kasar, inda binciken ya gano tsohon shugaban kai tsaye ya bai wa mutanen damar zama masu muhimmanci, sabanin bukatar kasar.

Bayan da aka mika masa rahoton a Pretoria, Shugaba Cyril Ramaphosa ya bayyana yadda abubuwan da ya kunsa za su taimaka wa Afirka ta Kudu ta ci gaba;

Ya ce , '' Mika wannan rahoto a hukumance na karshe a yau na nufin kammala matakin gyara da aka tsara a rahoto gudanar da bincike, kamar yadda mai bincike na kasar ya samar.''

''Nesa ba kusa ba rahoton ya dara bayanai na katutun cin hanci da rashawa, almundahana da saba ka'ida. Abu ne da kuma kasar za ta yi aiki ta hanysar ta tabbatar wadannan abubuwa ba su kara afkuwa ba.'' in ji shi

A yanzu dai hukumomin Afirka ta Kudun na aiki tukuru domin ganin an taso 'yan uwan na Gupta daga Hadaddiyar Daular Larabawa zuwa kasar domin tuhumarsu a kan laifukan da ake zarginsu da aikatawa

Babban mai Shari'a Zondo wanda ya shugabanci hukumar binciken ya kuma bayar da shawarar yin gyara a dokokin zaben kasar ta Afirka ta Kudu ta yadda, 'yan kasar za su rika zaben shugaban kasar kai tsaye maimakon jam'iyya da take yi a yanzu.

Ya ce wannan zai magance samun shugaba irin Jacob Zuba a kasar nan gaba.

Yanzu dai Shugaba Ramaphosa shi ne zai yanke hukunci ko za a sake daukar wani mataki na shari'a a kan wanda ya gada, Jacob Zuma.