Jacob Zuma: Cyril Ramaphosa karen farautar Turawa ne

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya yi wa Shugaba Cyril Ramaphosa kakkausar suka mai ban mamaki.
A cikin wata wasiƙa da aka kwarmata, Mista Zuma ya ce Shugaban da ya gaje shi ya butulce wa jam'iyyarsu ta ANC mai mulkin ƙasar, kuma yana yi wa turawan ƙasar aiki ne.
Wannan matakin na tsohon shugaban ƙasar ya bayar da mamaki, duk da cewa jam'iyyar ta ANC ta dare gida biyu saboda rikicin cikin gida.
Mista Zuma ya kuma zargi shugaban ƙasar da wofintar da kaburburan "matasa maza da mata da jami'an tsaron gwamnatin nuna bambancin launin fata da ƴan barandansu suka kashe su".
Ya kuma ce Mista Ramaphosa na butulcewa jam'iyyar ta ANC domin ya tsira da rayuwarsa.
Kuma ya ce shugaban na son ruguza jam'iyyar ne domin ya miƙa ƙasar ga ƴan kasuwa fararen fata.
Sakin wannan wasiƙar a wannan lokacin yana da tasiri.
Mista Zuma na fuskantar tarin tuhume-tuhume na aikata ba dai-dai ba, musamman na cin hanci da rashawa, kuma ana daf da kammala shari'ar da ake masa wadda aka daɗe ana yinta.
Amma akwai kuma wani babban taron kwamitin ƙoli na jam'iyyar da zai wakana a ƙarshen wannan makon, kuma ɓangaren da ke goyon bayan Mista Zuma zai so a kwamitin ya goya ma sa baya.
Cikin ƴan kwanakin nan, Shugaba Ramaphosa ya soki batun cin hanci da rashawa cikin jam'iyyar, har ta kai ga ya ce jam'iyyar ta ANC ce abar tuhuma ta farko.
Saboda haka babu mamaki da ake nuna ma sa fushi.
Amma abin lura shi ne: Ayyukan jami'an tsaron ƙasar sun fara razana wasu mutane masu ƙarfin faɗa-a-ji a Afirka ta Kudu.











