Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tantance gaskiya: Tsofaffin bidiyon da ake yadawa masu haifar da barazanar kai hari a Najeriya
- Marubuci, Fauziyya Tukur
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sashen tantance gaskiya na BBC
- Lokacin karatu: Minti 4
Jita-jitar da ake yadawa kan tsaron Najeriya da kuma babban zaben da ke tunkaro kasar na tasiri sosai a shafukan sada zumunta. Kuma masu amfani da waɗannan shafukan na yaɗa labaran cikin gaggawa - lamarin da ke ta'azzara rabuwar kawunan da ake samu saboda addini ko kabilanci.
"Fulani" maza da mata na ƙera bindiga
Wani bidiyo da ke nuna rukunin mutane da suka hada da maza da mata riƙe da makamai suna rawa da wakoki na yawo a shafukan sada zumunta irin su Facebook da WhatsApp a Najeriya.
Ana ikirarin cewa mutanen Fulani ne da cikin nishadi ke ƙera bindigogi. Wani mai amfani da shafin Tuwita ya wallafa bidiyon yana mai cewa: "Fulani na mallakar AK-47 yayin da ake fada wa 'yan kudanci su mallaki katin zaɓe... A yi tunani a kai".
An sake wallafa sakon nasa na Tuwita sama da sau 500 kuma an kalli bidiyon sama da 6,000.
Bincike ya nuna cewa an naɗi bidiyon ne a Ethiopia kuma mutanen da ke cikin bidiyon 'yan kabilar Afar ne.
Matar da ke jagorantar wakar, da ke rike da lasifika, tana sanye da tuta mai launin shudi, da fari, da kore da ja makale a gefen hijabinta. Tutar alama ce da ke nuna turjiya ta kabilar Afar da ke Ethiopia.
Duk da cewa mutanen da ke bidiyon na kama da Fulani daga Najeriya, wakar da suke yi ba ta harshen Fulani ba ce.
Bidiyon da ke nuna motar Dangote na jigilar gomman Fulani zuwa yankin kudu maso gabas
Akwai labaran karya da ake yaɗawa kan jigilar gwamman Fulani daga arewa zuwa gabashin Najeriya, da wata motar tirela ta kamfanin Dangote ke jigilarsu a bidiyon da ake yadawa, an nuna an tsayar da motar a shingen binciken 'yan sanda da kuma wasu rukunin 'yan sanda, da jami'an Kwastam da na Farir-kaya na kewaye da motar.
An nuna tarin maza a cikin tirelar, da aka rufe samanta da yadi mai kauri, suna tsaye.
An jiyo daya daga cikin jami'an tsaro da ba ya sanye da kaki yana cewa direban tirelar ya yi karya kan abin da ya kwaso a cikin tirelar lokacin da aka tsayar da shi.
"Lokacin da muka tsayar da su, direban ya shaida mana cewa gishiri ya dauko," kamar yadda aka jiyo shi yana cewa.
Bincike ya nuna cewa an naɗi bidiyon ne tun a ranar 8 ga watan Mayun 2020 a lokacin dokar kulle ta korona a Najeriya.
A lokacin, an takaita zirga-zirgar mutane amma ana iya dakon kayan abinci daga wani yanki zuwa wani - shi ya sa mazan suka ɓuya a cikin tirelar.
Jami'an tsaro a bidiyon duk na sanye da takunkumi, wanda ke nuna cewa an naɗi bidiyon ne a lokacin da ake tsaka da annoba da sanya takunkumi ya zama tilas kuma mutane na amfani da shi sosai.
Wani ƙarin binciken ya nuna cewa lamarin ya auku ne a karamar hukumar Awgu, a iyakar da ke tsakanin Abia da Enugu a kudu maso gabashin Najeriya.
Shaidu sun tabbatar da cewa motar tirelar na hanyar zuwa Fatakwal da ke kudancin Najeriya daga arewaci, wanda ya sha bamban da labarin karyar da ke cewa suna wannan balaguro ne daga arewa zuwa yammaci, kuma mazan Fulani ne.
Sai dai binciken namu bai iya gano ƙabilun mutanen da ke cikin tirelar ba a bidiyon mai tsawon minti uku.
Ikirarin da ake yi cewa Fulani na hanyar zuwa kudanci domin kaddamar da hari kamar yadda wannan bidiyo ke nunawa ba gaskiya ba ne.
Sakon barazanar da ake aikawa coci-coci da ke umartarsu su rufe
Wani bidiyo na wani jami'in ɗan sanda a taron manema labarai yana ta yaduwa a shafukan sada zumunta, musamman WhatsApp, inda aka jiyo yana cewa an ajiye wasikar barazana a kusa da "hedikwatarsu" kuma wasikar na ankarar da ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya da Coci-coci domin su rufe coci-cocinsu.
Bincike ya nuna cewa bidiyon ba sabo ba ne kuma an naɗe shi ne a 2021 bayan wasu 'yan bindiga sun aike da sakon barazana ga coci-coci a jihar Zamafara da ke fama da hare-haren 'yan fashin daji da sace mutane domin neman kudin fansa.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda ta jihar, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da cewa an naɗi bidiyon ne a Nuwambar 2021 ba wai na yanzu ba ne, kamar yadda masu amfani da shafukan sada zumunta ke yadawa.
Dan sanda da aka nuna a bidiyon Kwamishinan 'yan sanda ne a Zamfara, CP Ayuba Elkanah.
Amma a shafukan sada zumunta ana yada bidiyo dauke da rubutun da ke cewa: "Yan sanda sun tabbatar da samun wasikar barazana da ke umartar dukkanin coci-coci a Najeriya su rufe na tsawon wata uku".
'Yan bindiga a ranar Lahadi 5 ga watan Yuni 2022 sun kai hari wani coci da ke Owo, a jihar Ondo inda suka kashe aƙalla mutum 40 da jikkata da dama.
Labaran karya da bi-ta-da-kulli da ake yadawa na tasiri wajen ingiza hare-hare da ci gaba da yaduwarsu a shafukan sada zumunta na haifar da fargaba da fusata mutane a ƙasar.