Zaben fitar da gwani na APC: Labaran ƙarya da aka yaɗa a kansa

Lokacin karatu: Minti 4

An yi ta yaɗa labaran ƙarya kafin da lokacin da kuma bayan kammala zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, a daidai lokacin da ƴan ƙasar suka mayar da hankali kan lamarin da zai zama tamkar shimfiɗa ga zaɓukan watan Fabrairun 2023.

An yaɗa hotuna da bidiyo na ƙarya a shafukan sada zumunta da muhawara.

Batun shirin zaɓar mataimakin ɗan takara Musulmi da Bola Tinubu na APC ke yi a matsayinsa na ɗan takara Musulmi, wanda tuni ya ƙaryata, na daga cikin waɗanda aka yaɗa.

An yaɗa labarin ne a ƙoƙarin kawo ruɗani a tsakanin al'ummar ƙasar da kuma zuzuta bambancin addini.

Bidiyon Atiku da gwamnonin APC

Jim kaɗan bayan sanar da nasarar Bola Tinubu a zaɓen fitar da gwanin APC, an yaɗa wani bidiyo na TikTok a Facebook a wani shafi da aka sa masa suna: Support Nigerian Military.

Bidiyon ya nuna ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar da shugaban majalisar dattijai Ahmed Lawan da wasu ƴan APC da kuma gwamnonin APC din a wani falo.

Bidiyon ya nuna kamar suna wata ganawa ce, an jiyo ɗaya daga cikinsu yana cewa da Hausa "Mu koma babban falon".

An wallafa bidiyon tafe da wani saƙo da ke cewa "Wadannan su ne mutanen da suka zaɓi Bola Tinubu ɗazun nan a zaɓen fitar da gwani, amma cikin ƙasa da awa 24 ga su nan suna tare da ɗan takarar jam'iyyar adawa da zai fafata da shi."

An wallafa bidiyon fiye da sau 500.

Bayanai sun nuna cewa wani shafi mai suna Boboske1 ne ya fara ɗora bidiyon a TikTok ranar 23 ga watan Janairun 2022 ba tare da bayani ba.

Sannan kuma a ranar 22 ga watan Janairun 2022 ma Atiku Abubakar ya wallafa hotunan da aka ɗauka a irin wannan yanayin dai.

Kuma tufafin jikinsu duk irin na bidiyon ne sannan a falon da aka ɗauki bidiyon aka yi hotunan.

Abin da Atiku ya rubuta a kan hotunan shi ne cewa an ɗauki hoton ne lokacin da suka je yi wa Dahiru Barau Mangal ta'aziyyar rashin mahaifiyarsa a Katsina, ba taron siyasa ba ne kamar yadda saƙon Facebook ɗin ya ce.

Atiku ya zauna a falo ɗaya da Sanata Ahmed Lawan da wasu gwamnonin APC irin su Mai Mala Buni na jihar Yobe da Aminu Bello Masari na Katsina da Muhammad Badaru Abubakar na Jigawa a gidan Mangal a Katsina don yi masa ta'aziyya.

An yaɗa bidiyon da nufin jawo ruɗani da ƙara ta'azzara ƙabilanci da bambancin siyasa a Najeriya.

An yaɗa wasu bidiyon ma da dama a shafin Facebook ɗin da ya wallafa na farkon.

Jakunkunan kuɗin da aka ce Bola Ahmed Tinubu ya raba wa daliget

Wani mutum Maku Julius ya sake yada wani bidiyon a Facebook da ke nuna wata mata sanye da tufafin ƙabilar Yarbawa mai launin fari da kore da jakankunan 'Ghana Must Go' a gabanta.

An jiyo ta tana cewa cikin Turanci "wannan kyautar ta mutum ɗaya ce kawai" sannan ta ci gaba da bayyana cewa tana halartar wata liyafa ce ta wani Ajibola.

Bidiyon ya kuma nuna wata tirela maƙare da jakunkuna ana sauke su. Sai kuma aka jera jakunkunan a ƙasa a kusa da mutane a wani waje mai kama da wurin ajiye motoci.

Ana iya ganin mata da maza sanye da anko kamar na biki. Sai dai ba a ganin abin da ke cikin jakar.

An sanya wani take na ARASHOW a kan bidiyon. Sannan sai aka sake sanya wani taken kamar haka "DALIGET BOLA AHMED TINUBU YA SHIRYA MUKU."

Sannan Maku Julius ya sanya take a bidiyon mai cewa "Abin mamaki! Harkar kuɗi.... Sayen mutane." An kalli bidiyon kusan sau 1,000.

Binciken da muka yi ya gano cewa Arashow wani mai shirya biki ne kuma fitaccen mai amfani da shafin Instagram.

Yawancin bidiyon da ke shafin Arashow na ɗauke da irin tambarin da ke kan ɗaya bidiyon da aka yaɗa a Facebook.

Ta hanyar yin amfani da shafin matambayi-ba-ya-ɓata na Google an gano cewa tun watan Janairun 2022 aka fara yada bidiyon sannan jaridun Najeriya da dama sun yi labarin bikin saboda yawan kyaututtukan da aka raba.

An yaɗa bidiyon ne da gangan don a yaudari mutane su yarda cewa ɗan takarar shugaban ƙasar na APC ya rarraba wa daliget kyaututtuka don su zaɓe shi, bayan kuwa a wajen wani biki ne a Legas aka dauki bidiyon.

Saƙon tes na ƙarya daga Rochas Okorocha

An yaɗa hoton wani saƙon tes da aka ce ya fito ne daga wajen ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na APC wato Sanata Rochas Okorocha, aka yi ta yaɗa shi WhatsApp.

Duk da cewa ana iya ganin sunan wanda ya tura saƙon a jikin hoton, amma sunan Mr Okorochas aka rubuta a ƙarshen tes ɗin.

Saƙon yana zargin ɗaya daga cikin ƴan takarar saya wa sauran ƴan takarar fom don su janye masa a wajen taron, inda ya bai wa ko wannensu naira miliyan 500.

Saƙon ya kuma gargaɗi daliget da kar su zaɓi "ɓarayin da ba su da isasshiyar lafiya da ke amfani da motocin ɗaukar kuɗi don kai kuɗaɗe gidajensu."

Mutane da dama sun fassara saƙon da cewa da Bola Ahmed Tinubu wanda ya ci zaɓen ake.

An yi ta yaɗa jita-jita a kan batun lafiyarsa a ko ina a ƙasar. Sannan mutum bakwai ne suka janye wa Tinubu a filin zaɓen.

Saƙon na cike da kura-kuran rubutu, alama da ke nuna cewa an ƙirƙire shi ne kuma an yi shi cikin gaggawa.