Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
‘Haɗa ɗan takara da mataimaki Musulmai a Najeriya ya saba wa Musulunci’
Wani malamin addinin Musulunci a Najeriya ya ce haɗa mabiya addini ɗaya su kasance Shugaban ƙasa da Mataimaki a ƙasar mai al'ummar Musulmi da Kirista, ya saɓa wa ƙa'idar addinin Musulunci.
A hirarsu da BBC, Sheikh Halliru Abdullahi Maraya, wanda tsohon mai bai wa gwamnan jihar Kaduna shawara ne kan harkokin addinin Musulunci, ya ce adalci shi ne a tafi tare da mai kowanne addini wajen gudanar da mulkin ƙasa.
Malamin ya ce a mulki gaba daya ba abin da ke sa a samu a nasara illa a yi adalci.
Ya ce," Shi addinin Musulunci addini ne da yake so a koyaushe a yi wa wadanda ba sa yinsa adalci kuma a kyautata musu, ma'ana a ba wa kowanne mai hakki hakkinsa."
Sheikh Halliru Maraya, ya ce,"Najeriya tamu ce da Musulmi da wadanda ba Musulmi ba, don haka Kirista ya tabbatar cewa ya yi wa Musulmi adalci, haka shi ma Musulmi ya tabbatar ya yi wa wanda ba Musulmi ba adalci."
Ya ce a mataki na iko addinin Musulunci ya tanadi cewa a yi wa kowa adalci, kada kiyayya ta mutane ta sa a daina yin adalci, don haka ya kamata a yi mulki ta yadda za a tafi da kowa in ji shi.
Malamin ya ce a wajen kafa shi kansa mulkin, ya kamata a ga adalci ya fito baro-baro, kada wani bangare ko wani sashe su kwashe komai baki daya.
Malamin na kalaman ne a dai-dai lokacin da rahotanni ke cewa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na shirin ɗauko Musulmi daga arewacin ƙasar don mara baya ga ɗan takararta na shugaban ƙasa wanda shi ma Musulmi ne.
A don haka malamin ya ce, idan ya zamana shugaba Kirista ne, to a tsari na adalci sai ya zamana cewa mataimakinsa ba Kirista ba ne, haka in aka samu shugaba Musulmi ma to sai ya zamana mataimakinsa ba Musulmi ne ba.
Ya ce " Idan ana samun cewa masu addini iri guda su rinka shugabanci a kasa, to a gaskiya daya addinin da ba a yi da shi zai ce ba a yi masa adalci ba, kuma yin haka zai haifar da rashin hadin kai a kasa, za a yi ta samun tashin-tashina za a yi ta samun asarar rayuka da dukiya."
Karin bayani
Tun bayan kammala zabukan fitar da gwani na wadanda za su yi wa jam'iyyun siyasa a Najeriya takarar shugaban kasa, ake ta ce-ce-ku-ce a kan batun zabar wadanda za su yi wa 'yan takara mataimaka musamman a manyan jam'iyyun kasar biyu PDP da APC.
Idan aka yi la'akari da wanda ya samu takarar shugaban kasa a jam'iyya mai mulkin kasar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya kasance Musulmi daga kudu, wanda ake gani dauko mataimaki daga arewa zai zamo mishi babban kalubale.
Batun Kirista ko Musulmi zai dauka, ya zamo babban abin muhawara a tsakanin al'ummar Najeriyar.
Akwai dai rahotanni da suka ambato manyan arewacin kasar na masa hannunka-mai-sanda a kan cewa daukar Musulmi mataimaki zai fi ba shi damar samun nasara musamman a yankin, a inda Kiristoci kuma ke cewa hakan ba za ta sabu ba wai bindiga a ruwa.
Kafofin yada labarai dai sun ambato shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN, a Najeriya Dakta Samson Ayokunle, na gargadin cewa daukar mataimaki Musulmi ga dan takara Musulmi, mataki ne da ka iya zama tamkar wani bala'i ga kasar.
Tarihin Shugaban Kasa da Mataimakinsa Musulmi;
A tarihin siyasara Najeriya sau daya ne aka taba samun dan takarar shugaban kasa Musulmi da shi da mataimakinsa. Wannan kuwa ya faru a lokacin zaben 12 ga watan Yuni, 1993.
A lokacin marigayi Moshood Kashimawo Abiola (MKO) ne ɗan takarar shugaban ƙasa na SPD, Baba Gana Kingibe kuma mataimakinsa.
Zaɓen ya kasance ne tsakanin Social Democratic Party, SDP, da National Republican Convention, NRC, wadda marigayi Bashir Othman Tofa da mataimakinsa Sylvester Ugoh suka yi wa takara.