Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ta yaya jam'iyyu ke zabar mataimakan 'yan takarar shugaban kasa a Najeriya?
Bayan da jam'iyya mai mulki ta APC a Najeriya ta fitar da wanda zai yi mata takarar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa, yanzu ta bayyana karara kan 'yan takarar da manyan jami'iyyun siyasar kasar biyu za su fafata a zaben na badi.
To sai dai kafin a kai ga zaben, wani abin da zai dauki hankali a 'yan kwanaki masu zuwa shi ne wanda ko wannensu zai zaba a zaman mataimakinsa.
Kasa da mako biyu kenan da babbar jam'iyyar adwa ta PDP ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin wanda zai mata takara.
Sai kuma a ranar Laraba da jam'iyya mai mulki ta APC ta tsayar da tsohon gwamnan Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin nata dan takarar.
Haka ma sabuwar jam'iyyar NNPP ta tsayar da tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso, yayin da ranar Alhamis da daddare ne ake rufe tsayar da yan takara kamar yadda jadawalin INEC ya nuna.
Sai dai yanzu hankali zai koma ne wurin ganin wadanda jam'iyyun za su zaɓa a matsayin mataimakansu.
Wannan mataki na da tasiri sosai kan makomar kowace jam'iyya, lura da yadda tsarin Najeriya yake.
Kusan kowace jam'iyya na dauko shugaba ne daga yanki mataimaki kuma daga wani yankin.
Alal misali, lura da cewa kasar na da bangaren Arewaci da kuma Kudanci, yanzu haka shugaba mai ci wato Muhammadu Buhari ya fito ne daga yankin Arewaci, yayin da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya fito daga Kudu.
Hakan na nufin ko yanzu akwai yiwuwar irin wannan hada karfi ne jam'iyyun za su yi don ganin kowane daga manyan bangaroran biyu ya samu wakilci.
A yanzu aikin da ke gaban jam'iyyar APC shi ne na zabar wanda zai yi wa dan takararta Bola Tinubu mataimaki, yayin da PDP za ta nema wa Atiku Abubakar mataimaki.
Hakan na nufin akwai yiwuwar APC ta dauki mataimaki daga Arewaci, ita kuwa PDP ta dauko daga Kudu.
Kazalika NNPP da ta tsayar da Rabi'u Musa Kwankwaso akwai yiwuwar ta dauko nata mataimakin daga Kudanci.
Ta yaya jam'iyyu ke zabar dan takarar mataimakin shugaban kasa?
Abubuwa da dama ne jam'iyya ke dubawa kafin ta fitar da wanda zai mara wa dan takararta na shugaban kasa baya.
Da farko dai ba mataki ba ne da mutum daya zai dauka. Masu ruwa da tsaki a jam'iyya sukan tattauna tsakaninsu kafin cimma matsayar wa za su zaba.
Sai dai ba a nan gizo ke saƙar ba, don masu sharhin siyasa a Najeriya na ganin duka manyan jam'iyyun na da babban ƙalubale a gabansu wurin zabar wanda zai mara wa ɗan takararsu a zaɓen na 2023.
Malam Bashir Baba Muhammad na ganin babban kalubalen na ga dan takarar jam'iyya mai mulki wato Bola Tinubu na zabar wanda zai yi masa mataimaki.
"A nan Arewa dai kam ya zama wajibi gare shi ya duƙufa ka'in-da-na'in wajen nemo wani wanda zai karɓu, Arewa ta ji cewa tana da wakili."
"Gaskiya Bola Ahmed Tinubu zai fuskanci babban kalubale a Arewa," In ji Bashir Baba Muhammad.
Mai sharhin na kuma ganin cewa ita ma jam'iyyar adawa ta PDP na da nata kalubalen na cewa daga wane bangaren Kudancin kasar ne za ta dauko mataimaki, la'akari da tasirin da kabilanci da bangaranci ke da shi a can.
Wani kalubalen kuma da ke gaban manyan jam'iyyun shi ne kokarin kaucewa zabar tikitin Musulmi da Musulmi, wanda hakan zai hana daukar sanannun yan takara da ke da goyon bayan al'umma a kasar.
Wasu daga cikin wadanda ake tunanin Tinubu zai zaba
Dan takarar jam'iyyar APC Bola Tinubu ya fito ne daga Kudanci, saboda haka ana kyautata zaton zai dauki mataimaki ne daga Arewaci.
To amma wane bangare na Arewacin, la'akari da cewa akwai Arewa maso Yamma, da Arewa maso Gabas da kuma Arewa ta Tsakiya?
Wasu masu sharhin kuma na ganin irin rawar da gwamnoni suka taka wurin zamowarsa dan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar, zai sa su iya bukatar sa da ya dauki daya daga cikinsu.
Amma kuma wasu na ganin Tinubu da jam'iyyar APC za su yi gaban kansu ne su dubi wanda suke ganin zai iya kawo musu kuri'a da za su iya cin zabe ba tare da duba addini ko bangaren da ya fito ba.
Sai dai ita kuma jam'iyyar PDP mai adawa kamar yadda wasu masu sharhin ke gani, za ta fi samun matsala ne a yankin Kudu maso Yamma.
Dalili kuwa shi ne, dama suna neman a ba su takara yanzu kuma ga Tinubu sun samu. Saboda haka da wahala wata jam'iyya ta zabo mataimaki daga can ya yi wani tasiri.
Sai kuma batun shin daga Kudu maso Yamma za su dauko mataimakin ko kuma Kudu maso Gabas?
APC da PDP
Sai dai duk da cewa har yanzu ba a gama sanin wadanda za su yi wa manyan jam'iyyu takarar mataimakan shugaban kasa ba, akwai sunayen da ake ganin su ne gaba gaba da ake ganin a cikinsu ne za a zaba.
A bangaren APC akwai gwamnoni kamar su Simon Lalong na jihar Filato da Nasir El-Rufa'i na Kaduna da Kuma Muhammad Badaru Abubakar na Jigawa.
Akwai kuma gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, da kuma tsohon gwamnan Benue George Akume.
A bangaren PDP kuwa a makon da ya gabata an yi ta rade-radin cewa jam'iyyar da dan takararta Atiku Abubakar na shirin daukar tsohon gwamnan Imo Emeka Ihedioha.
A zaben 2019 Atiku Abubakar ya zabi tsohon gwamnan Anambra ne wato Peter Obi, wanda a bana ana dab da zaben fid da gwani ya fice daga jam'iyyar zuwa Labour Party.
Sai dai kawo yanzu babu ko da jita-jitar wa NNPP da ta zabi Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin shugaban kasa za ta zaba a matsayin mataimaki.