Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben 2023: Wasu 'ya'yan manyan kusoshin Najeriya da suka yi nasara a zabukan fitar da gwani
An kamala zaɓukan fitar da gwanaye na jam'iyyun siyasa a Najeriya, a matakin gwamnoni da ƴan majalisar dokoki na jiha da na tarayya da ƴan majalisar dattijai.
Kazalika babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta kammala nata zaɓen fitar da gwanin har a matakin shugabana ƙasa, yayinda jam'iyya mai mulki ta APC za ta yi nata a mako mai kamawa.
Za a iya cewa zaɓukan sun wuce amma sun bar ƴan Najeriya da ci gaba da tattauna yadda suka kasance, tun daga matakin rawar da daliget suka taka, da ma yadda wasu manyan masu riƙe da muƙamai suka sha ƙasa.
Sannan an ga yadda wasu sabbin ƴan takarar da suka kasance ƴaƴan wasu ƙusoshin ƙasar suka yi nasarar lashe wasu matakai na zaɓukan fitar da gwanin, yayin da wasu takwarorin nasu kuma suka sha kaye.
A wannan maƙalar, za mu yi duba kan wasu ƴaƴan wasu manyan ƙusoshin Najeriya da suka yi nasara a zaɓukan fitar da gwanaye na jam'iyyun siyasar ƙasar.
Umar Ganduje (Abba)
Umar Abdullahi Umar Ganduje wanda aka fi sani da Abba, ɗa ne ga gwamnan jihar Kano.
Ya yi nasara a takarar majalisar wakilai a mazaɓar Tofa da Rimin Gado da Dawakin Tofa a ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Abba ya lashe zaɓen ne ba hamayya, bayan da ɗan majalisa mai ci a yanzu Junaidu Yakubu ya janye masa.
A wani bidiyo da ya yaɗu a intanet jim kaɗan bayan nasarar tasa, an ga Umar Ganduje yana yi wa magoya bayansa alƙawura cewa zai samar wa matasa ayyukan yi, sannan kuma muradun al'ummar mazaɓarsa za su kasance kan gaba.
Bello El-Rufai
Bello El-Rufai, ɗan gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya yi nasara a takarar ɗan majalisar dokokin tarayya a jam'iyyar APC na Kaduna ta Arewa.
Bayan yin nasarar tasa, wata ƙungiya da ke goyon bayansa ta wallafa wani saƙo a Tuwita.
"Muna farin cikin sanar da ku cewa mun yi nasara a zaɓen fitar da gwani na takarar majalisar wakilai na Kaduna ta Arewa a ƙarshin jam'iyyar APC.
"A yayin da muke shiga zango na gaba na yaƙin neman zaɓe, muna roƙonku da ku yarda da mu, ku taya mu yaƙin neman zaɓe don mu sake ciyar da ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa gaba."
Mustapha Sule Lamido
Mustapha Sule Lamido, ɗa ne ga tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida a lokacin Shugaba Obasanjo kuma tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido.
Ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani na gwamnan jihar Jigawa ƙarƙashin jam'iyyar PDP.
A baya yayin wata hira da BBC, Sule Lamido ya ce ba laifi ba ne idan ya goyi bayan ɗansa ya tsaya takara inda ya ce duk wani mahaifi yana son ɗansa.
Abba Ahmad Sani Yariman Bakura
Sannan akwai Abba Ahmad Sani Yariman Bakura, ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara kuma tsohon ɗan majalisar dattijai, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, shi ma ya tsaya takarar dan takarar majalisar tarayya.
Abba Ahmad ya yi nasarar lashe zaɓen ne na mazaɓar Bakura da Maradun a jihar Zamfara, ƙarƙashin jam'iyyar APC.
An taɓa ba shi takarar ɗan majalisar jiha a 2019 amma daga baya kotu ta rusa dukkanin kujerun da APC ta ci.
Muhammad Abacha
Muhammad Sani Abacha, ɗan tsohon shugaban ƙasar Najeriya Janar Sani Abacha ma ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar PDP a jihar Kano.
Muhammad Abacha ya yi nasara ne da ƙuri'a 736 inda abokin karawarsa Ja'afar Sani kuma ya samu ƙuri'a 710.
Sai dai ga Muhammad, ba wannan ne karo na farko da ya taɓa tsayawa takarar ba, ya taɓa yin takarar a ƙarƙashin jam'iyyar CPC.
A yanzu Muhammad zai kara ne da Nasiru Gawuna na PC da Abba Kabir Yusuf na NNPP da Malam Ibrahim Khalil na ADC da kuma Salihu Tanko Yakasai na PRP.
Idris Abiola-Ajimobi
Idris Abiola-Ajimobi ɗa ne ga tsohon gwamnan Oyo marigayi Abiola Ajimobi of Oyo, kuma suruki ne ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Ya yi nasarar zama ɗan takarar majalisar dokokin jihar na mazaɓar Ibadan South-West II a ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa ɗan tsohon gwamnan ya yi nasara ne babu hamayya bayan da aka yi sulhu aka bar masa takarar.
Idris Ajimobi ay gode wa magoya bayansa da suka tabbatar ya yi nasara tare da ɗaukar alkawuran da jam'iyya za ta yi alfahari da shi.
Erhiatake Ibori-Suenu - ƴar James Ibori
Erhiatake Ibori-Suenu, ƴa ce ga tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori.
Ta tsaya takarar majalisar wakilan tarayya a mazaɓar Ethiopeon a PDP, kuma ta yi nasara a zaɓen fitar da gwani da ƙuri'a 46 bayan da ta doke abokin karawarta Ben Igbakpa wanda ya samu ƙuri'a 22.
Ta yi wannan nasara ce bayan da aka yi amannar cewa gwamnan jihar mai ci ya fi goyon bayan abokin karawar tata.
Usman Mamuda Shinkafi
Usman Mamuda Shinkafi, ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Mamuda Aliyu Shinkafi da ya nemi takarar dan majalisar dokokin jihar ta Zamfara ne.
Mahaifinsa ya yi mataimakin gwamna na shekara takwas, sannan ya yi gwamna an shekara huɗu.
Usman ya yi takarar ne ƙarƙashin jam'iyyar APC a mazaɓar Shinkafi.
Surajo Ibrahim Tanko
Surajo Ibrahim Tanko ɗa ne ga alkalin alkalan Najeriya Mai Shari'a Ibrahim Tanko da ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani na kujerar ɗan majalisar dattijai ta Bauchi ta Arewa a jam'iyyar APC.
Ibrahim matashi ne da yake da shekara 40 da ƴan kai. Ya fafata da mutum huɗu ciki har da sanata mai ci Alhaji Adamu Bulkachuwa.
Surajo Tanko ɗan asalin ƙaramar hukumar Giade ne a gundumar Katagum da ke jihar Bauchi.
Sani Ibrahim Tanko
Sani Ibrahim Tanko shi ma ɗa ne ga alkalin alkalan Najeriya kuma ƙani ga Surajon.
Ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani na takarar ɗan majalisar wakilan tarayya a mazaɓar Shira da Giade a jam'iyyar PDP.
A yanzu Sani zai fafata ne da ƴan takara daga jam'iyyar NNPP da kuma na jam'iyyar APC mai ci.
Sharhi
Ko da yake a baya wasu 'ya'yan gwamnoni da ma shahararrun 'yan siyasa sun nuna sha'awarsu ta tsayawa takara, amma a wannan karon adadinsu ya karu, abin da masana harkokin siyasa ke kallo a matsayin yunkuri na gadar iyayensu.
Masana harkokin siyasa dai na ganin irin wannan mataki da 'ya'ya da kuma dangin gwamnoni da manyan 'yan siyasa suke dauka na fitowa takara a matsayin maras alfanu ga dimokuradiyya.
Sai dai akwai waɗanda suke ganin ba za a ce babu alfanu gaba ɗaya ba, musamman ganin cewa mafi yawan ƴan takarar matasa ne da ake ta fafutukar ganin suna ɗare muƙamai a madafun iko a ƙasar.