Dalilin da ya sa Ukraine ta fusata da hukumar sa ido kan makamin Nukiliya ta MDD

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin makamin nukiliya na Ukraine, ya zargi shugaban hukumar da ke sa ido kan makamin nukiliya a Majalisar Dinkin Duniya da yin karya kan shirin kai ziyara cibiyar makain ta kasar Rasha.
A ranar Litinin ne Rafael Grossi, ya ce Ukraine ta gayyaci hukumar International Atomic Energy Agency cibiyar makamin nukiliyar da ke Zaporizhzhia.
Sai dai kamfanin Energoatom, ya ce babu wani goron gayyata da aka kai, sannan duk wata ziyara za ta nuna halaccin zaman Rasha a wurin.
Mr Grossi ya kira zargin da karya tsagwaronta. "Lokacin yaki muke, don haka akwai sosa rai kuma mutane su na daukar bangaranci," ya fadi haka a hirarsa da BBC.
Sai dai ya yi ikirarin hukumarsa na da damar kai ziyara domin duba tsaron cibiyar, sannan ziyarar ba ta bukatar goron gayyatar da za a iya zuwa yanzu ko kuma babu damar tsawaita ta.
Babban kamfanin makamin nukiliyar Ukraine Energoatom, ya fitar da zazzafar sanarwa cikin fusata a ranar Talata tare da zargin Mr Grossi da makaryaci, ta hanyar ikirarin kasarsa ce ta bukaci ya kai ziyarar. Sanarwar ta ci gaba da cewa wannan ziyara tamkar halasta abin da ya kira "halasta mamayar da Rasha ta yi wa kasarsa".
Kamar yadda kafar yada labaran Rasha ta bayyana, hukumar IAEA na tattaunawa da hukumomin kasar kan yiwuwar wannan ziyara.
Dakarun Rasha sun karbe iko da cibiyar makamin nukiliya ta Zaporizhzhia, wadda ita ce mafi girma a yankin Turai, a farkon watan Maris , kwanaki kadan da mamaye Ukraine.
Kasashen duniya na ta kiraye-kirayen a dauki mataki, bayan luguden wutar da dakarun Rasha suka yi wa cibiyar bayan karbe iko da ita.
Duk da cewa an ci gaba da gudanar da aiki a cibiyar, kuma babu wasu manyan gine-gine da aka lalata a cibiyar, sannan yanayin wurin na nan yadda ya ke. Ma'aikata 'yan Ukraine sun ci gaba da aiki a cibiyar amma bisa umarnin Rasha.
Wata da watanni kenan Mr Grossi na nuna damuwa kan tsaro a Zaporizhzhia, tare da cewa ya na son jagorantar wata tawaga domin kai ziyara Ukraine.
A dai ranar Talata hukumar IAEA ta sanar da cewa komai na tafiya yadda ya dace a cibiyar Chernobyl, wadda a makwannin da suka gabata ke karkashin ikon Rasha, kuma a karon farko Ukraine ta karbe cikakken ikon tafiyar da ita.
Bayanai sun sun tabbatar da cewar cibiyar na aiki yadda ya dace tamkar watannin da suka gabata kafin Rasha ta mamaye Ukraine.










