Rikicin Rasha da Ukraine: Rasha ta bai wa dakarun Ukraine wa'adin awanni su yi saranda

Rikicin Rasha da Ukraine

Asalin hoton, AFP

Rasha ta shaida wa sojojin Ukraine na karshe da suka rage a birnin Mariupol da take yi wa ruwan bama-bamai cewa za su tsira da rayukansu idan suka mika wuya cikin sa'o'i masu zuwa.

Moscow ta ce dakarunta sun kawar da duk wasu sojojin turjiya daga birnin, baya ga share baraguzai daga hanya.

Sanarwar da ma'aikatar tsaron Rasha ta fitar ta bayyana yanayin da ake ciki a a matsayin bala'i.

Ta ce ta yi tayin mika makaman ne a wani mataki na nuna dattaku da mutunta rayuka.

A ranar Asabar ne shugaba Zelensky ya yi gargadin cewa za a kawo karshen tattaunawar zaman lafiya idan Rasha ta kashe sauran sojojin.

Magajin garin Mariupol ya yi kiyasin cewa akalla fararen hula dubu ashirin ne suka mutu a tsawon makonni ana kai hare-hare ba kakkautawa.

"Putin zai iya amfani da nukiliya"

Nina Krushcheva

Asalin hoton, Nina Krushcheva

Jikar tsohon shugaban rusasshIyar tarayyar Soviet Nikita Khrushchev ta shaida wa BBC cewa Shugaba Vladimir Putin na iya yin shirin amfani da makaman kare-dangi a fagen fama idan har ya zama dole don samun nasara a yakin Ukraine.

Nina Krushcheva, wacce farfesa ce a harkokin kasa da kasa dake birnin New York, ta ce shugaban na Rasha yana ganin kansa a matsayin na baya-bayan nan a cikin jerin jagororin Rasha masu karfi, tun daga Peter the Great.

Ta ce ta yi matukar kaduwa da irin zaluncin da wasu sojojin kasar Rasha ke yi a kasar Ukraine, musamman ma a wuraren da dakarun Checheniya masu kawance ra Rasha ke kai harehare.