Ukraine: Muhimmancin birnin Mariupol da ke 'tsakiyar yakin' kasar

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Daga Tom Bateman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Zaporizhzhia, south-eastern Ukraine
Ana samun karuwar alamu da ke nuna cewa Rasha ka iya karbe iko da daukacin birnin Mariupol, da sojinta suka yi wa kawanya wanda ke kudancin tashar ruwan Ukraine, da yakin makwanni shida ya daidaita.
Jami'ai a rundunar tsaron Ukraine sun ce suna ci gaba da turjewa da nuna jajircewa, za kuma su ci gaba da haka musamman sojin da ke kasa. Sai dai sun ce akwai yiwuwar Moscow za ta yi kokarin karbe iko da birnin, yayin da 'yan a-waren da ke mara wa kasar baya ke cewa Mariupol na gab da fadawa hannunsu.
Su ma sojin Ukraine sun fara korafin cewa suna fuskantar karewar alburusai, kuma an yi amanna sun fara tura su baya zuwa wasu yankuna kebantattu da suka hada da gabar ruwan Mariupol.
Babu wanda ya san makomar birnin da yaki ya daidaita. Ga Rasha, za ta samu damar mallake yankin daga kudanci zuwa gabashi wanda ke iyakokinta. Za ta girke dakarun da za su kare muradinta, sannan su bai wa Shugaba Vladimir Putin daddadan labari na yin nasara a bangaren farko na kaddamar da mamayarsa.
Wannan zai zama babban koma-baya, kamar yadda shugaban Ukraine ke bayyana Mariupol da "ruhin yakin da ake yi a yau".

Asalin hoton, Anadolu Agency via Getty Images
A farkon watan Maris ne sojin Rasha suka kewaye Mariupol, suka yi masa kawanya, lamarin da ya janyo kashe dubban farar-hula, da sanya wadanda suke raye fadi tashin da wadanda suka makale a birnin ke ciki.
Dubban mutane sun tsere zuwa arewaci, inda suke tafiyar sayar da rai ta hanyar wucewa ta fagen-daga. A nan a Zaporizhzhia, na ga yadda farar-hula ke tudadowa a kowacce rana, sun bayyana irin bala'i da masifun da ke faruwa a birnin.
A kwanakin baya, an yi tsammanin sojin Rasha za su danna su raba Mariupol gida biyu, wadanda za su kare shi da mayakan, kamar yadda binciken kungiya mai nazari kan sha'anin yaki ta bayyana.
An yi amanna an fatattaki sojin Ukraine zuwa tashar ruwa da kamfanin Azovstal inda ta nan suka fara kaddamar da hare-hare a makwannin baya.
Wani bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna mayaka kamar na birget 36, inda suka sha alwashin ba za su mika wuya ba.
"Za mu jajirce, ba za mu gajiya ba, ba za mu mika birninmu ba," in ji wani da ya bayyana a bidiyon da kafar talbijin din kasar a ranar Talata.
''Amma ainahin abin da ke faruwa a birnin da aka yi wa kawanya, ba ma samun alburusai sannan babu ko abinci.'' Wani bangare na bidiyon ya nuna shi a kusa da jiragen ruwa, da wani daki da ya yi kama da na karkashin kasa. Daya daga cikin wanda ke dakin karkashin kasar ya na dogarawa da sanda.
Abin da aka wallafa a shafin Facebook a ranar Litinin, ya bayyana halin da suke ciki da ''karshe a matakin yakin, ga wasunmu mutuwa ce, wasu kuma kame su za'a yi,'' in ji wanda ke bidiyon, ya kara da cewa ''babu hanyar komawa baya, sojin Rasha kuma sun mana kawanya.''
Wani mai sharhi kan lamuran Ukraine ya yi nazarin bidiyon inda ya ce mai yiwuwa da gaske ne ko akasin haka, musamman ikirarin da aka yi cewa masu kutse sun karbe ikon shafin. Amma sama da awa 36 bidiyon yana nan ba a cire shi ba.
Kawanyar da aka yi wa Mariupol, da katsewar sadarwa sun taka muhimmiyar rawa wajen gaza samun bayanai da rahoton halin da ake ciki a birnin.
Akwai shakku kan cewa sojin Ukraine na cike da kishirwar makamai da alburusai da abinci da ruwan sha.

Asalin hoton, Anadolu Agency via Getty Images
Rahotanni sun bayyana cewa sojin Ukraine na kokari cikin makonnin da suka gabata domin ganin sun kai wa takwarorinsu kayan aiki ciki har da gilashin da ke ganin nesa dare da rana, batiran da za su rika caji, da makari daga hare-haren roka, sai dai lamarin babu sauki a ciki.
"A taikace, birnin a kewaye yake kuma cikin kankanin lokaci aka yi masa kawanya, babu wata dama ta kai kayan agaji, kamar yadda Justin Bronk, babban jami'i a cibiyar a binciken sha'anin yaki ta Royal United Services Institute (RUSI) a Amurka ya ce.
"Sun dade suna rike da kambun, sun yi kokari kuma babu wanda ya yi zaton hakan za ta kasance. Da wuya a fadi tsahon lokacin da za a kwashe cikin wannna matsalar. Sun yi yar kankanuwar nasara ta wata fuska daban,'' in ji shi.
Kokarin Ukraine na kwashe wadanda suka ji rauni, da wadanda suke son ficewa daga Mariupol, ya ci tura.
Makwanni biyu da suka gabata, ma'aikatar tsaron Rasha ta yi ikirarin ta harbo helikwaftan yaki na Ukraine mai lamba Mi-8, nisan kilomita 5 daga tashar da kamfanin Azov ya ke.
A ranar Talata, sun yi ikirarin sama da sojin Ukraine 100 sun yi ta fafatawa domin su fita daga kamfanin tama da karafa, amma sai dai an kashe kusan rabi daga cikinsu ta hanyar ruwan makamai atilari da makamai masu linzami, ya yin da sama da 40 suka mika wuya.
A bidiyon da ya saba yi wa 'yan kasa jawabi a ranar Talata, shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce: "Kacokom makomar Ukraine ta danganta ne ga karfi da jajircewar da muka nuna. Makomarmu baki daya da biranenmu da kauyuka da garuruwanmu duka na hannun mu.
"Ina mika godiya ga daukacin 'yan kasarmu da suka fahimce ni. Wadanda suka ki yarda da shan kaye, a daidai lokacin da muke ganin sakamakon kamar da wuya. Saboda a ko da yaushe duhu ne ke fara zuwa kafin haske ya mamaye shi.
"Ina son shaidawa zakakuranmu, wadanda ke cikin mawuyacin hali. Wadanda ke tsare Mariupol. Bataliya ta 36, da dakaru na musamman, da ofireshan 12, da dakaru na musamman da ke gadin Ukraine. Dakarun da ke kula da iyakokinmu, da ma'aikatan sa kai mussan na"Right Sector". Da asibitin soji na 555, har da rundunar 'yan sandan kasarmu."
Masu gadin teku ban barku a baya ba, da jami'an tsaron Mariupol da bataliyar Azov, har da kungiyoyin da suka dauki makamai a shekarar 2014 wanda suka sauya da rikidewa cikin jami'an tsaron birnin Kyiv, da suka zama kashin bayan tsaro a kasarmu.
Wadannan wani dan bangare ne na jami'an tsaron Ukraine, Sai dai ganinsu a wannan wuri ya sanya Moscow ci gaba da yada farfaganda, alamun da ke nuna su na da amfani, su na daga cikin wadanda suka fara maida martani lokacin da aka fara mamayarmu, da sojin Rasha suka kira ''atisayen soji'' tare da ikirarin an yi domin karbar 'yancin wasu yankuna da akai ikirarin ba na mu ba ne.''
A wani bangare kuma, rahotanni daga jami'an tsaron yankin sun ce Rasha ta fara girke makamai masu guba a Mariupol a makwannin da suka gabata, sai dai ba a tabbatar da wannan ikirari ba. Sai dai kamar matashiya ce kan yadda yakin ka iya munanan da zama hadari nan gaba.
Yanayin yadda aka kwace iko da kusan daukacin birnin, alamu ne da ya nuna yadda sojin Rasha su ke kokarin kare shigar da duk wani abu da za a shiga da shi Mariupol, ko fita da shi, musamman ta yammacin yankunan Donbas, inda Moscow ke kara zafafa kai hare-haren fatattakar duk wani burbushin dan Ukraine da mallake shi.
Za kuma a iya ganin yadda Moscow ke kara samun karfi a arewacin Mariupol, wanda daya ne daga cikin dalilan da suka sanya 'yan Ukraine suka ki bari a kore su ko karbe iko da mazauninsu, in ji Mr Bronk.
Ana ganin za a iya amfani da dakarun wajen sake kamewa da karawa sojin Rasha karfi a Kherson, inda sojin Ukraine ke ta kokarin karbe wasu yankunan, akwai alamun nasara amma ba sosai kamar yadda Ukraine ke fata ba.
Shugaba Zalensky, ya ci gaba da gangami da karfafawa sojin Uktraine da ke Mariupol, wadanda ke tsakiyar yakin. "Idan zukatanmu suka yi rauni, su ka daina bugawa yadda ya kamata, hakan na nufin za a ci mu da yaki, don haka kar mu karaya," in ji Zalensky.













