An ba Jamusawa tikitin jirgin kasa na euro tara kan tsadar makamashi

Asalin hoton, Reuters
Daga nan zuwa watanni uku masu zuwa, Jamusawa za su dinga balaguro da tikitin euro tara, kwatankwacin naira 6,000 a kowanne wata, domin rage musu radadin tsadar rayuwa.
Shirin da gwamnati ta kirkira, ya hada fannin sufuri ta mota, da jirgin kasa da na karkashin kasa da motocin bas, amma ban da jirgin kasa da ke fita daga wata jiha zuwa wata.
Manufar samar da tikitin mai rahusa, shi ne bai wa masu motoci kwarin gwiwar barinsu a gida.
Har wa yau, an rage senti 30 na harajin kowacce lita guda ta man fetur, lamarin da ya sanya farashin lita daya ya kama kasa da yuro 2, farashin dizel ma an rage da centi 14 kan kowace lita.
Wannan mataki dai an dauke shi ne, bayan shugabannin kasashen Turai sun tattauna, kuma za su sake nazari akan kara wa'adin nan da watanni uku masu zuwa.

Asalin hoton, EPA
Ministan sufurin Jamus, Volker Wissing, ya bayyana rage farashin tikitin zuwa euro 9 wata babbar dama ce ga 'yan kasa. ''Kawo yanzu mun saida tikiti sama da miliyan bakwai, wannan abin farin ciki ne."
Saidai kuma kamfanonin jiragen kasa kamar Deutsche Bahn, na fuskantar matsaloli sakamakon cinkoson mutane, da tsaikon tafiyar jirage da uwa uba soke wasu da ke zuwa sassa daban-daban na birane da garuruwa, hakan ya sanya miliyoyin fasinjoji ke sukar sabon shirin na gwamnatin Jamus.
A watan Afirilu da ya wuce, kashi 70 cikin 100 na jiragen da ke balaguro mai nisa su na barin tashoshin jiragen kasa akan lokaci, amma masana na cewa tashoshin na aikin kashi 80 ne kawai. Daga fara saida wannan tikiti a ranar Laraba, babu wani korafi da aka samu kan tashin jiragen kasa.
Kamar sauran kasashen duniya, ita ma Jamus na fuskantar kalubalen tashin gwauron zabbin makamashi, inda tsadar kayan masarufi ta kai kashi 7.9 a watan da ya gabata.
A ranar Laraba ne shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya shaidawa 'yan majalisar dokokin kasar cewamamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, ita ce sanadin tashin farashin kusan manyan abubuwan da aka fi amfani da su a duniya, da suka hada da kayan abinci, da makamashi da sauransu.











