Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
AMVCA 2022: Stan Nze da Osas Ighodaro ne suka lashe gwarazan kyautar
Yayin bikin karrama 'yan wasan fina-finan Afirka ta Africa Magic Viewers Choice Awards (AMVCA), Stan Nze da Osas Ighodaro ne suka yi nasarar zama gwarzo da gwarzuwar tauraro na shekarar 2022.
Ms Osas wadda 'yar Najeriya ce mai shaidar zama 'yar ƙasar Amurka ta doke 'yan wasa kamar Kehinde Bankole, da Bisola Aiyeola, da Nancy Isime da sauransu wajen lashe kyautar a ɓangaren dirama. da fim ɗinta mai suna "Rattlesnake".
Nze wanda shi ma ya fito a fim ɗin Rattlesnake: The Ahanna Story, ya doke Timini Egbuson, da Gabriel Afolayan, da Femi Jacobs.
Fim ɗin ne dai ya ba wa Darakta Ramsey Nouah kyautar gwarzon mai ba da umarni.
Sauran 'yan wasan da suka lashe kyautuka na AMVCA su haɗa da Funke Akindele, da Samuel Perry (Broda Shaggi).
Fim ɗin tarihi mai suna "Amina" ne ya lashe kyautar gwarzon fim.