Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
IPOB: Buhari yana ziyarar aiki a Jihar Ebonyi
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Jihar Ebonyi a kudancin ƙasar a wata ziyarar aiki ta kwana biyu da yake yi.
Ya sauka a Babban Filin Jirgi na Akanu Ibiam da ke Jihar Enugu, inda ya ƙarasa zuwa Uburu da ke cikin Ƙaramar Hukumar Ohanzara a Jihar Ebonyi.
Gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi da takwaransa na Ebonyi David Umahi ne suka tarɓi shugaban tare da sauran manyan ƙusoshin gwamnati.
Ana sa ran Buhari zai ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Umahi ta aiwatar, wanda yanzu haka yake neman jam'iyyarsu ta APC ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ce titunan jihar sun cika maƙil da jami'an tsaro daban-daban.
Shugaban na ziyarar ce a yayin da masu neman ɓallewa daga Najeriya ke kara kaimi wajen kai hare-hare kan ofisoshin 'yan sanda da wasu hukumomin gwamnatin tarayya da ma mutane a jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Hari na baya-bayan nan shi ne wanda suka kai kan wasu sojoji biyu da ke shirin aure a karshen makon jiya a Jihar Imo.
An fille kawunan mutanen ne a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar domin yin bikin aurensu na gargajiya.
Rundunar sojin kasar ta zargi mayakan kungiyar IPOB da hannu wajen kai harin, tana mai shan alwashin "tabbatar da hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan aiki."
Shi ma Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da kisan sojojin, kuma ya umarci jami'an tsaro su gurfanar da masu laifin a gaban kotu.
Sai dai kungiyar ta IPOB ta musanta kai hari da kashe sojojin.
A wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya yi ta'aziyya ga rundunar sojin Najeriya da kuma iyalan Warrant Officer Audu Linus da kuma Private Gloria Mattew waɗanda aka fille wa kawuna bayan an harbe su.
Ya alaƙanta kisan da dabbanci, inda ya ce wannan aika-aika ta saɓa wa al'adu da zamantakewa.
Haka kuma shugaban ya yi kira ga jagororin al'ummomi da na yankuna da na ƙasa baki ɗaya da su yi "magana da murya ɗaya domin nuna cewa Najeriya ƙasa ɗaya ce kuma al'umma ɗaya, wadda ba ta goyon bayan abin da ya kira kisan dabbanci".
Shugaba Buhari ya bayar da umarni ga sojojin ƙasar da sauran hukumomin tsaro da su gano da kuma hukunta waɗanda ke da hannu a wannan aika-aika.