Gobara ta kashe mutane da dama a haramtacciyar matatar fetur a Jihar Imo

Mutum fiye da 50 ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wasu haramtattun matatun man fetur biyu da ke Jihar Imo a kudancin Najeriya.

Hukumomi a jihar sun faɗa wa BBC cewa waɗanda lamarin ya ritsa da su za su iya zarta hakan saboda har yanzu ana ci gaba da aikin kwashe gawarwakin mutanen da suka ƙone ƙurmus.

Gobarar ta tashi ne a matatun da ke kusa da juna a Ƙaramar Hukumar Ohaji-Egbema ranar Juma'a da dare bayan fashewar wani abu.

Wutar ta ƙone akasarin mutanen ta yadda ba a iya gane su. Waɗanda lamarin ya ritsa da su sun haɗa da masu gudanar da matatar da kuma wasu mazauna yankin.

Babu tabbas kan abin da ya haddasa gobrar ya zuwa loƙacin haɗa wannan rahoton.

Kwamashinan Albarkatun Man Fetur na Imo Goodluck Opiah ya kai ziyara wurin, yana mai cewa "ba zan iya faɗa muku adadin mutanen da suka mutu ba saboda mutane sun zo sun tafi da wasu 'yan uwansu".

Kazalika, kwamashinan ya ayyana mamallakin matatar a matsayin wanda hukumomi ke nema ruwa a jallo.