Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me jam'iyyun siyasa a Najeriya ke yi da miliyoyin kuɗin fom?
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
Masu bin kafofin yaɗa labarai a Najeriya da waɗanda ma ba sa bi sun kwana da labarin naira miliyan 100 a matsayin kuɗin sayen fom na tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar.
Farashi mafi ƙaranci a APC shi ne na naira miliyan biyu da masu son tsayawa takarar majalisar jiha za su biya.
Ita ma babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta saka miliyan 40, yayin da mai neman takarar majalisar jiha zai biya kuɗi mafi ƙaranci na 600,000.
Tsohon Gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso ya sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP kan naira miliyan 30.
Sai dai jam'iyyun na cewa akwai sassaucin farashi ga matasa da kuma mata da ke son tsayawa takarar.
Shin me jam'iyyun ke yi da waɗannan miliyoyi bayan sun karɓe su? Mun tambayi tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP na Ƙasa Sanata Ibrahim Tsauri da tsohon Sakataren Walwala na Ƙasa na APC Ibrahim Masari don sanin hakan.
Farashin fom ɗin PDP
- Shugaban ƙasa: kuɗin na-gani-ina-so miliyan biyar + kuɗin fom miliyan 35
- Gwamna: kuɗin na-gani-ina-so miliyan ɗaya + kuɗin fom miliyan 20
- Majalisar dattijai: kuɗin na-gani-ina-so 500,000 + kuɗin fom miliyan uku
- Ɗan majalisar wakilai: kuɗin na-gani-ina-so 500,000 + kuɗin fom miliyan biyu
- Ɗan majalisar jiha: kuɗin na-gani-ina-so 100,000 + kuɗin fom 500,000
Kwamatin Gudanarwa na PDP ya yi wa matasa 'yan shekara 25 zuwa 35 da kuma mata, ragin kashi 50 cikin 100 na farashin fom ɗin.
Farashin fom na APC
- Shugaban ƙasa: kuɗin na-gani-ina-so miliyan 30 + kuɗin fom miliyan 70
- Gwamna: kuɗin na-gani-ina-so miliyan 10 + kuɗin fom miliyan 40
- Majalisar dattijai: kuɗin na-gani-ina-so miliyan uku + kuɗin fom miliyan 17
- Ɗan majalisar wakilai: kuɗin na-gani-ina-so miliyan ɗaya + kuɗin fom miliyan tara
- Ɗan majalisar jiha: kuɗin na-gani-ina-so 500,000 + kuɗin fom miliyan ɗaya da rabi
APC ta ce mata da kuma masu buƙata ta musamman za su biya kuɗin na-gani-ina-so, amma za a ba su fom ɗin takara kyauta a muƙamin da suke nema.
Su kuwa matasa 'yan ƙasa da shekara 35 za su biya kuɗin na-gani-ina-so amma za su samu ragin kashi 40 cikin 100 na farashin fom ɗin da suke so.
Wane ne ke ƙayyade farashin fom?
A jam'iyyar APC, Kwamatin Gudanarwa wato National Working committee, shi ne ke da alhakin daddale farashin fom na kwane mataki.
"Bayan sun kammala kuma sai ya miƙa wa Kwamatin Zartarwa (National Executive Committee) wanda zai shi ba shi izinin fara sayarwa," a cewar tsohon Sakataren Walwala na Ƙasa na APC Ibrahim Masari.
Wa ake ba wa kuɗin fom?
Da zarar jam'iyyu sun daddale farashin fom ɗin takara 'yan takarar za su fara lalo kuɗi domin sayen sa.
Tsohon Sakataren PDP na Ƙasa Sanata Ibrahim Tsauri ya ce a jam'iyyarsu sakataren kuɗi ne ke tara kuɗaɗen fom ɗin da aka saya.
"Daga baya kuma sai ya tura wa ma'aji don ya ajiye," in ji shi.
Wane ne ke ba da fom?
Har wa yau, idan 'yan takara sun biya kuɗin fom ɗin a wajen sakatare, za su karɓi fom ɗin ne daga wajen sakataren tsare-tsare na ƙasa.
Wa ke kasafta kuɗin?
Bayan an tattara kuɗaɗen za a kai wa majalisar gudanarwa ta jam'iyya, inda 'yan kwamatin za su kasafta abubuwan da za a yi da su, a cewar Sanata Tsauri.
"Su waɗannan 'yan kwamatin ba albashi ake biyan su ba...saboda ba kodayaushe ake samun kuɗin ba, amma idan an samu sai a ware wa kowane ofis kuɗin gudanarwarsa.
Me ake yi da kuɗaɗen?
Bai wa ɗan takara kuɗin kamfe: A jam'iyyar PDP, daga cikin abubuwan da ake yi da kuɗin sayar da fom har da bai wa 'yan takara kuɗin gudanar da kamfe.
Tsohon sakataren na PDP ya ce idan aka zo takara, jam'iyya za ta bai wa ɗan takara "maƙudan kuɗaɗe don ci gaba da kamfe".
"Ɗan takara shi ne wanda aka yi zaɓe ya samu tikitin takara, ba mai son yin takara ba," a cewarsa.
Shi ma Ibrahim Masari na APC ya ce jam'iyyarsu ta bai wa dukkan 'yan takara "gudunmawa mai tsoka" don yin kamfe a kowane mataki.
Kare jam'iyya a kotu: Kazalika, Masari ya ce ana amfani da kuɗin wajen ɗaukar lauyoyin da za su kare jam'iyya a kotu idan aka kai ta ƙara.
Biyan albashi da kuɗin gudanarwa: A cikin waɗannan kuɗaɗe kuma ake biyan albashin ma'aikata da kuma gudanar da ayyukan yau da kullum.
"Misali, mu a PDP muna shan man disel na miliyan biyu duk wata a ofisoshinmu biyu. Sannan kuma akwai kuɗin ruwa da na wuta. Kusan kullum akwai abin da za a biya."
Shirya babban taro na ƙasa: Jam'iyyun siyasa a Najeriya kan shirya babban taro na ƙasa bayan na jihohi da kuma na shiyya.
A wurin tarukan ne kuma ake zaɓar shugabannin jam'iyyun da za su ja ragamarsu. Jam'iyyun na amfani da kuɗaɗen da suka samu na sayen fom din ne wajen shirya su.
Sauran hanyoyin da jam'iyya ke samun kuɗi
Baya ga kuɗaɗen sayar da fom, jam'iyyun siyasa a Najeriya kan samu kuɗi ta hanyar sayar da katin shaidar jam'iyya.
"Abin da ya sa kuke ganin katin shaidar jam'iyya kyauta ne, wani lokacin gwamna zai iya sayen katin jam'iyya kamar 500,000 ya raba wa mutane," in ji Sanata Tsauri.
Ibrahim Masari ya ce akwai haraji da ya kamata kowane ɗan jam'iyya ya dinga biya, wanda ake ajiyewa a asusun jam'iyya.
"Ya zuwa lokacin da muka sauka daga mulki, mun bar kusan naira biliyan huɗu a asusun APC," in ji shi.